Turkiyya ta aika wa Afghanistan kayayyakin taimako

Acikin wannan wata mai alfarma na Ramadana Turkiyya ta rabawa mabukata kayayyakin abinci na ton 40 ga iyalai 750 a jahohin Herat da Nimruz a kasar Afghanistan

1422359
Turkiyya ta aika wa Afghanistan kayayyakin taimako

Acikin wannan wata mai alfarma na Ramadana Turkiyya ta rabawa mabukata kayayyakin abinci na ton 40 ga iyalai 750 a jahohin Herat da Nimruz a kasar Afghanistan.

Kodinetan hukumar Hadin Kai da Taimako ta kasar Turkiyya (TİKA) a Herat, Ali Ergun Çınar, ya bayyana cewa a wani watan azumi suna rabawa mabukata kayayyakin abinci a yankin, inda ya kara da cewa a wannan shekarar sun kara yawan kayayyakin da suke rabawan.

Çınar, ya kara da cewa sun raba ton din abinci 40 ga iyalai 750 da kuma ga marayu, dalibai, nakasassu da makamantansu a jihar Herat da Nimruz.Labarai masu alaka