Wakar Opera ta farko a Turkiyya

Ko kun san cewar Mustafa Kamal Ataturk da kansa ne ya bayar da umarnin a rera wakar Opera ta farko ta Turkiyya?

1422079
Wakar Opera ta farko a Turkiyya

Ataturk ya bayar da matukar muhimmanci a zamaninsa ga wakoki tare da girmamama mawaka. A zamnin shekarun farko na Jamhuriyar Turkiyya,kamar yadda ya bayar da muhimmanbci wajen tattalin arziki, ilimi, masana’antu da sauransu, haka ya ba wa harkar waka muhimmanci. A shekarar 1934 Ataturk ya nuna yana son a samar da wakar Opera ga Turkiyya.

Akwai dalili mai jan hankali da ya sa ya bukaci haka. A baya, shugaban Kasar Iran Ali Shah Pevlevi da tsarin bin Mazhaba ya janyo gaba a tsakanin al’ummar kasarsa, ya samu gaiyata zuwa Turkiyya. A lokacinda aka tabbatar da zai zo sai Ataturk ya bukaci a rera wakar Opera don girmamawa ga Shan Pevlevi a dare daya kuma shi ne ya zami me za a ce a cikin wakar ta Opera. Za a dauke daga rubutun masanin adabin Iran Firdaus. Munir hayri Egeli ne ya rubuta Libretto. Sai ya ba wa Ahmet Adnan Saygun mai shekaru 27. Saygın ya gama wannan aiki a cikin wata daya.

A karon farko a ranar 19 ga watan Yunin 1934 aka fara rera wakar ta Ozsoy Opera.

 Labarai masu alaka