Kefir mai sinadaran gina jikin dan adam

Ko kun san cewar abun sha na Kefir da ake yi a Turkiyya yana kara karfin garkuwar jikin dan adam?

1383527
Kefir mai sinadaran gina jikin dan adam

Shekaru dubu 5000 da suka gabata aka fara samar da Kefir daga nonon akuya a Tsakiyar Asiya inda yanzu ake shan sa a dukkan duniya. A yanzu ana kara nonon saniya ko na tunkiya wajen samar da Kefir. Kefir yana da sinadarai masu kara karfin garkuwar dan adam, kuma yana taimakawa wajen narkar da abinci da sauri wanda ake kuma maganin ciwukan kasa narkewar abinci da shi tsawon daruruwan shekaru da suka gabata.

Kefir da ke kara karfin garkuwar jikin dan adam tare da kara karfin yaki da cututtuka a jiki, yana da sinadaran hana mutum kamuwa da wasu cututtuka da dama. Yana maganin mummunar gajiya, damuwar da kuncin zuciya da saurin fushi. Yana hana jijiya yin tauri tare da kare kwanjin mutum daga narkewa. Masu matsalar kasa yin bacci ma za su iya shan sa don neman waraka. Amma masu ciwon garkuwar jiki ko gajiya da mutuwar jiki ya kamata su fara tuntubar likitansu kafin su sha Kefir.Labarai masu alaka