Abun sha na Boza mai amfani a jiki

Ko kun san cewa daya daga cikin abubuwan sha na Turkiyya mai suna Boza na daga cikin abubuwan sha mafi dadewa a duniya?

1383523
Abun sha na Boza mai amfani a jiki

Shekaru dubunnan da suka gabata ana amfani da Boza kuma wani abun sha ne na al’ada a Turkiyya. A yanzu ana shan sa a yankunan Daula Usmaniyya da na Asiya ta Tsakiya. A lokutan sanyi ba a hakura da Boza kuma a Turkiyya ana gabatar da shi tare da aya ruwan dorawa.

Ana samar da abun sha na Boza da garin acca, ruwa da sukari kuma an fi shan sa a lokacin sanyi. A cikin ana samun Lactic acid saboda kasancewarsa daga dangin abubuwansa sha na Fermente. Wadannan sinadarai suna da amfani ga jikin dana dam sosai. Suna kara karfin garkuwar jikin dan adam. Suna kara karfin jiki. Boza yana fitar da wasu datti da cututtuka da suka shiga jikinmu. Bpza yana kara karfi da gina jikin dan adam. Yana dauke da Vitamin B. Hakannya sanya ake shawartar masu sun yi kiba da su dinga sha, da ma matasa da suke girma da kuma wadanda suke fuskantar matsalar kasala da mutuwar jiki.

Boza yana da sinadarar gina jiki na tamin A, B da E da ma Calcium. Babban abunda ya kamata a kula da shi shi ne a tabbatar an samar da Boza ta tsaftatacciyar hanya.Labarai masu alaka