Shayin Ada da ke yin maganin cututtuka da dama

Kokun san cewa shayin Ada da ake nomawa a Turkiyya yana maganin cututtuka da yawa?

Shayin Ada da ke yin maganin cututtuka da dama

Shayin Ada suna ne na ganyen shayi da aka sani a kasashen yankin tekun Bahar Rum. Akwai jinsin irin wannan shayi har 900 a duniya. Akwai 97 a Turkiyya kuma 51 daga cikinsu an san su sosai tare da aöfani da su matuka gaya.

Ba za a iya kirga adadin amfanin da shayin Ada yake da shi ba wanda ya zama kamar wata mu’ujiza. Ana mafni da shi wajen magance ciwon hakori da kuma matsalar narkewar abinci. Sinadarin Antioxide dakecikinsa na taimakawa wajen karfafa garkuwar jiki. Binciken da aka gudanar ya bayyana cewar shayin Ada yana rage mummunar kiba da maikon jikin mutum. Yanakuma taimakawa wajen lafiyar kwakwalwa.

Duk da wannan fa’ida da shayin Ada yake da shi idan aka dade ana shan sa kuma da yawa to zai iya janyo wasu cututtukan. Ana bayar da shawarar mata masu ciki da shayarwa kar su sha shayin Ada mai karfi. Masu shan maganin cutar sukari ko kiba ma ana bukatar da su yi hankali sosai.

A Turkiyya shayin Ada ne aka fi amfani da shi a matsayin magani. Ana amfani da ganyensa wajen saka wa a Salad ko kuma abincikka masu nama da kifi domin kara kamshi. Ana kuma amfani da man da ake fitarwa daga jikinsa wajen samar da kayan kwalliya.

SİNYAL ...Labarai masu alaka