Amfanin furen Orkide

Ko kun san cewa ana amfani da ganyayen sama na furen Orkide wajen samar da abin sha na salebin da yake na musamman a Turkiyya?

Amfanin furen Orkide

A lokacinda aka ambaci Orkide abunda ke fara zuwa hankulan mutane shi ne furen da ake nomawa a kasashe masu zafi. A saboda haka idan aka kalli wannan abu za a ga Turkiyya kasar da aka fi nomar furen a tsakanin kasashen Gabas ta Tsakiya da na Turai.

A yankin Anatoliya ana ba wa furennin orkide sunan Salep ko Shalep. Kalmar Salep ta samo asali daga tsaffin kalmomin Anatoliya dake nufin waraka ko samun lafiya Tun daga dubunnan shekaru zuwa yau al’umar Anatoliya na kisar orkide da Salep saboda ana amfani da su wajen yin magani.

Kawai nau’ukan orkide kusan 140 a Turkiyya kuma ana amfani da kusan 40 wajen neman waraka. Ana mafni da ganyen saman wannan fure wajen samar da salep . A watannin Yuni da Yuli ne furen ke fitar da wasu ganyayyaki jajaye da ake amfani da su. Ana nika su tare da dafa su da madara a sha domin neman waraka. A gundumar Elbistan dake lardin Kahramanmaras aka fi noma wannan fure. Ana shan salep da ake samarwa daga furen sannan ana kuma zuba shi a ayiskrim din Maras don kara masa dandano.


Tag: Orkide

Labarai masu alaka