Bukukuwan sabuwar shekara a salo kala-kala

Ko kun san an yi bukin sabuwar shekara a kasashen duniya daban- daban ta hanyoyi kala-kala da bukukuwa iri daban-daban?

Bukukuwan sabuwar shekara a salo kala-kala

Sabuwar shekara dake nufin sabon abu a kowanne bangare, an yi bukintaa sassan duniya daban-daban da bukuku na’i kala-kala. Manufar dukkan bukukuwan shi ne sabuwar shekarar ta zama cike da alheri.

Bukin sabuwar shekara ne buki da aka sani mafi dadewa a duniya.Bukin sabuwar shekara na farko an yi shi ne shekaru dubu 4000 kafin Haihuwar Annabi Isha a kasar Babil. Farkon bazara shi ne sabuwar shekara a wajen babilawa.

Duk da babu wani ilimin tauraro da ya tabbatar da muhimmanci 1 ga Janairu, amma al’adun da suka amince da wannan kalanda suna murnar zagayowar sabuwar shekara a ranar.

A Turkiyya a ranar 26 ga watan Disamban 1925 aka karbi kalandar Miladiyya kuma a karon farko a shekarar 1926 aka fara bukin sabuwar shekara a kasar.

A shekarar 1935 aka ayyana 1 ga watan Janairu a matsayin hutu a kowacce shekara. Ana kuma buki da hutawa a daren wannan rana.Labarai masu alaka