Amfanin kiwon mage ga dan adam

Ko kun san kiwon mage na da amfanunnuka da dama ga lafiyar dan adam?

Amfanin kiwon mage ga dan adam

Malaman Kimiyya da suka gudanar da bincike kan alaka dan adam da dabbobi, sun gano kiwata mage na kara wasu abubuwa da dama ga lafiyar dan adam. Zama da mage a gida na kara karsashin zamantakewar mutum tare da kara yawan yin dariya da motsa jiki wanda ke rage damuwa. Hakan na kara karfin garkuwar jikin dan adam.

Daya daga cikin shaidun dake tabbatar da alakar mage da dan adam shi ne kwarangwal din wata mage mai shekaru dubu 9,500 dake tsibirin Cyprus wanda aka yi amfani da jirgin ruwa wajen kaita da muzuru 1 zuwa tsibirin wanda a aokacin babu mage a cikinsa. Wannan na nuna cewar a yankin Anadolu shekaru dubu 10,000 da suka gabata ana rayuwa tare da mage.

Daya daga cikin maguna masu kyau ita ce nau’in Magen Van wadda ke rayuwa a kusa da tafkin Van na Turkiyya. Wannan mage na da idanuwa ruwan shudi da ruwan zuma wanda ake ganin lalacewar ido ne. Tana da farar jela mai kama da ta dila da kuma gashi mai ba sna’awa. Tana son rua tare da kaunar ninkaya.


Tag: Amfani , Lafiya , Mage

Labarai masu alaka