Fina-finan kasar Turkiyya aka fi kallo a Nahiyar Turai

An bayyana cewa a shekarar 2019 an kalli fina-finan kasar Turkiyya a kasashen waje har sau miliyan 33.6

Fina-finan kasar Turkiyya aka fi kallo a Nahiyar Turai

An bayyana cewa a shekarar 2019 an kalli fina-finan kasar Turkiyya a kasashen waje har sau miliyan 33.6.

Sineman kasar Turkiyya da ta samawa kasar kudaden shiga har na dala miliyan 980 ta kasance wacce ta samu daraja mai gwabi a nahiyar.

A yayinda a shekarar bara aka kalli fina-fina kasar Turkiyya har sau miliyan 33.6 a cikin kasar, a kasashen waje kuwa an kalli fina-finan kasar har sau miliyan 25.9

Fina-finan kasar Turkiyya sun kasance wadanda aka fi kalla a Nahiyar Turai a cikin shekaru takwas da suka gabata. Kaso 55 cikin darin fina-finan da ake kallo a gidajen sineman Nahiyar Turai na kasar Turkiyya ne, kasar ta kare wadannan alkaluman a shekarar 2019.

 Labarai masu alaka