Gobara a gidan ajje namun daji dake Jamus

Sakamakon gobarar da ta kama a gidan ajje namun daji na Krefeld dake Jamus dukkan dabbobin dake gidan sun kone.

Gobara a gidan ajje namun daji dake Jamus

Sakamakon gobarar da ta kama a gidan ajje namun daji na Krefeld dake Jamus inda dabbobi da dama suka kone.

Sanarwar da mahukuntan gidan ajje namun daji na Krefeld suka fitar ta ce ibtila'in ya afku da daddare kuma gidan birrai ya kone kurmus.

Sanarwar ta ce sun tsorata sosai, babu wani biri da ya yi saura a gidan ajje namun dajin, kuma har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba.

Labaran da jaridun Jamus suka fitar na cewa sama da dabbobi 30 ne suka mutu.


Tag: Krefeld , Jamus , Zoo

Labarai masu alaka