Sunan 'Muhammad' ya shiga daya daga cikin sunaye 10 da aka fi sanyawa yara a Amurka

Alkaluman wata hukumar bincike mai suna "BabyCenter" dake Amurka sun bayyana cewar sunan Muhammad ya shiga cikin jerin sunaye 10 da aka fi saka wa jarirai maza a 2019 a Amurka.

BabyCenter ta fitar da rahoton shekarar 2019 game da sunayen da ake ba wa yara kanana a Amurka.

Rahoton ya ce a 2019 sunan Liam ne na farko sannan sai Noah,  Aiden, Grayson, Caden, Lucas, Elijah, Oliver da Muhammad ske biyo baya.

Rahoton ya kuma sake fitar da bayanai game da sunan da aka sanyawa yara mata a Amurka a 2019.

An bayyana cewar sunan Aliya na Musulmai ma ya shiga jerin sunayen mata 10na farko da aka fi sanawa jaririai mata a Amurka a 2019.

Alkaluman sun ce sunan Sophia ne na farko inda Olivia, Emma, Ava, Aria, Isabella, Amelia, Mia, Riley da Aliya suka biyo baya.Labarai masu alaka