Bukin bayar da lambar yabo na TRT World

Shirin "TRT World Citizen" na Gidan Radiyo da Takabijin din kasar Turkiyya mai taken "kyakkyawar sauyi da karfafawa" domin yi wa alumma hidima ya samu shekaru biyu da kafuwa

Bukin bayar da lambar yabo na TRT World

Shirin "TRT World Citizen" na Gidan Radiyo da Talabijin na kasar Turkiyya mai taken "kyakkyawar sauyi da karfafawa" domin yi wa al'umma hidima ya samu shekaru biyu da kafuwa.

A wannan shekarar ma za'a bayar da lamban yabo ga wadanda suka yiwa al'umma hidima a karkashin shirin TRT World Citizen.

Za'a gudanar da taron bayar da lamban yabon a lstanbul ga wadanda suka cancanta daga kasa da kasa a taron na bukin TRT World Citizen karo na biyu.

A ranar 28 ga watan Nuwamba ne za'a gudanar da taron tare da halartar matar shugaban kasar Turkiyya Emine Erdoğan.

A bukin za'a bayar da lambunan yabo ne a sassan ilimi, sadarwa, matasa, world citizen da sashen ci gaba da samun nasarori a rayuwa.

A shirin gajeruwar fim na wannan shekarar za'a haska fim mai taken "Savaşın Kadınları" watau Mata Mayaka.

Za'a baiwa wannan fim din kyauta kasancewar yadda ya nuna gwagwarmayan da mata suka dinga yi duk da sun samu kansu cikin mawuyacin hali.

Lamban yabo mafi girma shi ne wanda za'a baiwa wadanda suka samu nasarori a rayuwa. Haka kuma za'a bayar da lamban yabon na hidima ga al'umma ga Yusuf Islam.

Yusuf lslam zai bayyana sabuwar kungiyar bayar da tallafi mai suna 'Barış Treni' watau Jirgin Kasar Lumana karo na farko a daren bukin.

 

 Labarai masu alaka