Rana Irin ta Yau 24.05.2019

Muhimman abubuwan da suka faru a wannan rana.

Rana Irin ta Yau 24.05.2019

A ranar 24 ga watan Mayu shekara ta alif dari takwas da arba’in da hudu, Samuel Morse ya turo sako da rubutun da ya kirkiro mai suna “Mors Alphabet” a karo na farko daga Gidan ‘yan majalisar Amurka zuwa gidan jirgin kasan Baltimore.

A ranar 24 ga watan Mayu shekara ta alif dari tara da ashirin da hudu ne, hanyoyin jiragen kasa na Antoliya suka dawo hannun gwamnatin Tukiyya, inda da a hunnun ‘yan kasar waje suke.

A ranar 24 ga watan Mayu shekara ta alif dari tara da hamsin da shida ne, aka kaddamar da gasar wakar Eurovision a karo na farko a birnin Lugano inda ‘yar kasar Swizaland mai suna Lys Assia ta lashe gasar.

A ranar 24 ga watan Mayu shekara ta alif dari tara da  sittin da hudu ne, mutane 318 suka rasa rayukansu yayin kallon gasar kwallon kafa da aka yi tsakinin Peru da Ajantina, inda mutane kimanin 500 suka ji rauni.

A ranar 24 ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da uku ne, ‘yar Turkiyya Sertab Erener ya lashe gasar Eurovision da aka kaddamar a karo na 48 a kasar Litoniya, inda ta rera waka mai suna “Everyway That I can”.


Tag: Tarihi

Labarai masu alaka