Erdoğan ya shirya wa shugabannin duniya dina a lstanbul

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya ci abincin marece tare da baƙin da suka halarci buɗe kataɓaren masallacin Büyük Çamlıca dake lstanbul.

Daga cikin baƙin akwai shugabannin kasashe da kuma wakilan wasu shugabannin.

Erdoğan, ya gana da baƙin da suka zo daga ƙasashen Afganistan, Albeniya, Bosnia , Filistin, Gini, Kırgızistan, Nijer, Najeriya, Pakistan, Senegal, Somaliya da Tunisia.

Shugaban Erdoğan ya gana da shugaban kasar Albeniya llir Meta, na Gini Alpha Conde, Senegal Mackay Sall , firaministan Falasdinu Muhammad lbrahim lshtiye, shugaban tawagar Afghanistan Dr Abdullah Abdullah, jami'in Bosnia Shefik Caferovich, da kuma shugaban jin ra'ayin jama'a a majalisar Bosnia Bakir İzetbegovic.

 Labarai masu alaka