Gwamnatin Burundi ta hana bude wuraren Ibada a Bujumbura

Gwamnatin kasar Burundi ta haramta gina wa ko bude wuraren ibada da suka hada da Masallatai da Majami'u a Bujumbura Babban Birnin Kasar kuma mafi tsufa a cikinta.

Sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Burundi ta fitar na cewa, daga yanzu babu wani Masallaci ko Majami'a da za a bude a Burundi.

Sanarwar ta ce, masu son bude wuraren bauta su tafi wajen gari su yi hakan amma ba a Bujumbura ba.

Babu wata sanarwa Malaman Addinai suka bayar game da wannan mataki.

A 'yan watannin nan Majami'un Protestan na kara yawaita sosai a birnin mai mutane kusan miliyan 2.

Kaso 80 na al'umar Burundi Kiristoci ne inda kaso 10 kuma Musulmai.

Sakamakon sauye-sauyen da aka yi a farkon shekarar nan an mayar da Babban Birnin Kasar zuwa Gitega.Labarai masu alaka