Turkiyya na da burin zama cibiyar Ilimi ta duniya

Shugaban Hukumar Kula da Turkawa dake Kasashen Waje (YTB) Abdullah Eren ya bayyana cewa, nan da shekarar 2020 kasarsa na son zama cibiyar ilimi ta duniya inda za samu dalibai dubu 200 'yan kasashen waje dake neman ilimi a cikinta.

Turkiyya na da burin zama cibiyar Ilimi ta duniya

Shugaban Hukumar Kula da Turkawa dake Kasashen Waje (YTB) Abdullah Eren ya bayyana cewa, nan da shekarar 2020 kasarsa na son zama cibiyar ilimi ta duniya inda za a samu dalibai dubu 200 'yan kasashen waje dake neman ilimi a cikinta.

Eren ya yi bayani a wajen wani taro kan sha'anin Ilimi da Majalisar Dinkin Duniya inda ya bayyana irin aiyukan YTB da kuma kokarin da suke yi wajen bayar da tallafin karatu ga daliban kasashen waje.

Eren ya ce, an kafa Hukumar YTB a shekarar 2010 kuma tana da manufar tallafawa tare da kula da Turkawan dake rayuwa a kasashen waje tare. Haka zalika Hukumar na raya al'adu da tarihin da aka gada.

Eren ya tabo batun daliban Ƙasashen waje Dake karatu a Turkiyya tare da fadin irin tallafin da gwamnati ke ba su.

Ya ce, a duniya akwai daliban Ƙasashen waje sama da miliyan 7 dake karatu inda a Turkiyya ake da kimanin dubu 150 wanda adadinsu ya ninka sau 7 a cikin shekaru 10 da suka gabata.

Eren ya shaida cewa, daga cikin daliban Ƙasashen waje dake Turkiyya akwai dubu 17 da Hukumar YTB take ba wa tallafi.

Ya ce "Nan da shekarar 2020 Turkiyya na son zama cibiyar ilimi ta duniya inda kuma adadin daliban kasashen waje zai kai dubu 200 a cikinta."


Tag: YTB , Turkiyya , Eren

Labarai masu alaka