Za a saka tarihin cin hanci da rashawa a manhajar koyarwa a makarantun Malaysia

Ma'aikatar Ilimi ta Malaysia za ta saka batun handama da wawure kudaden kasar da tsohon Firaminista Necip Razak da wasu manyan 'yan siyasa suka yi a manhajar ilimi ta kasar.

Za a saka tarihin cin hanci da rashawa a manhajar koyarwa a makarantun Malaysia

Ma'aikatar Ilimi ta Malaysia za ta saka batun handama da wawure kudaden kasar da tsohon Firaminista Necip Razak da wasu manyan 'yan siyasa suka yi a manhajar ilimi ta kasar.

Ministan Ilimi na Malaysia Maszlee Malik ya bayar da amsa ga tambayar da dan majalisar adawa na jam'iyyar United Malay National Party (UMNO) Ahmad Maslan game da wannan batu.

A amsar da Malik ya bayar ya ce "Za su saka yadda Hukumar IMDB da wasu manyan 'yan siyasar kasar suka yi wa kasarsu fashi da mukami da tsakar rana a manhajar darasin tarihi ta yadda al'umar dake zuwa a nan gaba za su guji aikata hakan."

Minista Malik ya kuma ce, daga yanzu za a sake manhajar tarihi da ake amfani da ita tare da sabunta ta wanda a kan hakan za a kafa kwamiti mai karfi.

A sanarwar da tsohon Firaministan Najip razak ya yi a shafinsa na sada zumunta ya soki kalaman na Malik inda ya ce, wannan mataki zai siyasantar da harkokin ilimi a kasar.

Bayanan da aka samu a binciken cin hanci da rashawa kan yadda aka tafiyar da al'amuran Asusun Cigaba na Malaysia mai suna "1Malaysia Development Berhad (IMDB)" an gano yadda aka aika da kudi har dalar Amurka miliyan 681 zuwa bankuna, kamfanunnuka da asusun banki masu alaka da tsohon Firaminista Najip Razak.

Ofishin Mai Gabatar da Kara ya bayyana cewa, kudaden da aka samu a asusun mutane 5 kudi ne da wasu 'yan Saudiyya suka bayar da taimakon su, bayan Saudiyya ta tabbatar da hakan ne sai aka sanar da Najip Razak na da hannu a aikata cin hanci da rashawa.

An sake dawo da binciken da ake wa Najip bayan ya fadi zabe a ranar 6 ga watan Mayu.

Ana tuhuma tare da yi wa tsohon Firaministan shari'a kan laifuka har guda 30 bisa zargin cin hanci da rashawa.

Gwamnatin Malaysia dai ta bayar da sanarwar neman taimako daga 'yan kasar don farfado da tattalin arzikinsu da biyan basussukan da tsohuwar gwamnatin ta ciwo.Labarai masu alaka