Makarantar Darul Anwar ta Turkawa da ke Najeriya ta fara bayar da ilimi ga dalibai

Makarantar Darul Anwar ta Kasa da Kasa Mallakar Turkawa da ke Najeriya ta shiga sabuwar shekarar karatu bayan kayan taimakon da ta samu daga Turkiyya.

1070219

Fatih Emin Danisan na Kungiyar Adamder da Kawancen Abuja-Istanbul ya ce, shekaru 2 kenan da makarantar ta fara bayar da ilimi.

Ya ce, a wannan shekarar dalibansu sun kai 281. Snna biyan malaman makarantar, sayen litattafai da kayan karatu da sauran kashe kudade da taimakon da suke samu daga Turkiyya. 

Ya kara da cewa, a ranar Talatar nan ma sun raba wa daliban takalma, litattafai, alkaluma da kayan karatu bayan zuwan taimako daga Turkiyya.

Sakamakon matsalar kudade akwai yara da yawa da ba sa zuwa makaranta a Najeriya.

Alkaluman ma'aikatar Ilimi na cewa, akwai yara kusan miliyan 10.5 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya mai yawan mutane miliyan 200.Labarai masu alaka