Turkawa a ciki da wajen kasar na bukukuwan Ranar Nasara

Turkawa a cikin kasar da ofisoshin jakadancin Turkiyya a kasashen waje na gudanar da bukukuwan Ranar Nasara ta 30 ga watan Agusta.

zafer bayrami.jpg

Turkawa a cikin kasar da ofisoshin jakadancin Turkiyya a kasashen waje na gudanar da bukukuwan Ranar Nasara ta 30 ga watan Agusta.

A karkashin bukukuwan da za a yi, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai ziyarci Anitkabir da karfe 11 na rana.

Shugaba Erdogan zai kuma karbi sakonnin taya murna na Ranar Nasara a fadarsa inda zai kuma shirya cin abinci a fadar tasa ga daliban da suka kammala karatun digiri a kwalejin koyon yaki ta Turkiyya.

A Kutahya za a gudanar da bikin murnar Ranar Nasara a karkashin Ministan Matasa da Wasanni Mehmet Kasapoglu. 

Shugaba Mustafa Kamal Ataturk shekaru 96 da suka kabata ya ayyana samun nasarar korar wadanda suka so mamaye Turkiyya.

An kammala yakin da aka yia Dumlupinar.

A ranar 1 ga Satumba Mustafa Kamal Pasa ya bayar da umarni ga dakaru da su tsare gabar tekun Mediterrenean.Labarai masu alaka