An kashe 'yan sanda da dama a harin 'yan bindiga a Najeriya

A jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya an kashe 'yan sanda 13 a lokacin da suke yin sintiri.

1677589
An kashe 'yan sanda da dama a harin 'yan bindiga a Najeriya

A jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya an kashe 'yan sanda 13 a lokacin da suke yin sintiri.

Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun bayyana cewa, wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kan 'yan sandan da ke sintiri a kauyen Kurar-mota.

'Yan sanda 13 ne suka mutu sakamakon harin.

Kakakin gwamnan jihar Zamfara Yusuf Idris Gusau ya tabbatar da afkuwar lamarin amma bai ce komai ba game da adadin 'yan sandan da aka kashe. Gusau ya kara da cewa, gwamna Bello Matawalle ya ziyarci 'yan sanda 7 da aka jikkata sakamakon harin.Labarai masu alaka