Kenyatta ya ja kunnen masu kera makamai ba bisa ka'ida ba a Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi kira ga kamfanonin dake kera makamai ba bisa ka'ida ba, da su daina su kuma yi rajista ta yarda zasu ci gaba da ayyukansu bisa sabuwar tsarin da gwamnatin kasar ta fitar

1655571
Kenyatta ya ja kunnen masu kera makamai ba bisa ka'ida ba a Kenya

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi kira ga kamfanonin dake kera makamai ba bisa ka'ida ba, da su daina su kuma yi rajista ta yarda zasu ci gaba da ayyukansu bisa sabuwar tsarin da gwamnatin kasar ta fitar.

A cewar labarin jaridar The Daily Nation, Kenyatta, a cikin jawabinsa a wurin lalata muggan makamai da aka kame a yankin Kajiado a kasar, ya yi alkawarin yin afuwa ga masu kera makaman ba bisa ka'ida ba idan suka tuba suka mika wuya.

Da yake cewa makaman da ba a yi musu rajista ba da aka kama a Kenya na kayan gida ne, Kenyatta ya ce masu kera makaman za su iya barin ayyukansu kuma su yi aiki bisa ga sabuwar tsarin masana'antar kera makamai gwargwadon kwarewar su.

Kenyatta ya kara da cewa,

"Ina so na yi kira . A yanzu Kenya za ta iya kera kananan makamai, wadanda suka shagalta da kera makamai ba bisa ka'ida ba ya kamata su daina su kuma yi rajista ta yarda zasu cigaba da ayyukansu bisa tsarin sabuwar doka ta hanyar da zasu yi aikinsu ba tare da tsangwama ba ta kuma hanyar da za mu bunkasa tattalin arzikin kasarmu"

Kenya ta gina sabuwar masana'antar kera makamai a cikin watan Afrilu kan kimanin dala miliyan 36.Labarai masu alaka