Shugaban Kasar Uganda ya nada Ministoci 82

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni da ya sake lashe zabe ya nada Ministoci 82.

1655707
Shugaban Kasar Uganda ya nada Ministoci 82

Shugaban Kasar Uganda Yoweri Museveni da ya sake lashe zabe ya nada Ministoci 82.

An bayyana cewa, a sabuwar gwamnatin da aka kafa a Uganda akwai kananan Ministoci 50 da manya 32.

Museveni ya nada tsohuwar Ministar Lafiya Robinah Nabbanja a matsayin Firaminista, ya kuma nada matarsa Janet Museveni a matsayin Ministar Ilimi.

A ranar 14 ga watan Janairun 2021 ne Museveni ya sake lashe zaben Shugaban Kasar Uganda a karo na 6.

Museveni ya lashe zabuka a shekarun 1996, 2001, 2006, 2011, 2016 da 2021.Labarai masu alaka