Kwalara ta yi ajalin mutane 15 a Najeriya

Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Kano dake arewacin Najeriya.

1638063
Kwalara ta yi ajalin mutane 15 a Najeriya

Mutane 15 sun rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar kwalara a jihar Kano dake arewacin Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce, shugaban kauyen da lamarin ya faru Sulaiman Muhammad ya shaida mutuwar mutane 15 mafi yawansu kananan yara.

Muhammad ya kuma ce, an kwantar da wasu mutanen 40 a asibiti.

Sakamakon rashin kyakkyawan ruwan sha da rashin kula da lafiya yadda ya kamata cutar kwalara na yin ajalin mutane a Najeriya.

A kasar ana yawan samun cututtukan zazzabin cizon sauro, kyanda, tayfot, farankama da sauransu.

 Labarai masu alaka