An kashe mutane 9 a harin 'yan bindiga a Najeriya

Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a jihar Anambra da ke kudu maso-gabashin Najeriya.

1629028
An kashe mutane 9 a harin 'yan bindiga a Najeriya

Mutane 9 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a jihar Anambra da ke kudu maso-gabashin Najeriya.

Kakakin 'yan sandan Anambra Tochukwu Ikenga ya bayyana cewa, an aika da jami'an tsaro zuwa yankin da lamarin ya faru.

Ikenga ya kara a cewa, an shawo kan al'amura a yankin.

Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun ce, mutane 19 aka kashe sakamakon harin.

A gefe guda, an aiyana dokar hana fita waje a yankin sakamakon lamarin.Labarai masu alaka