An rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar

A Yamai Babban Birnin Nijar, an rantsar da sabon Shugaban Kasar Mohamed Bazoum a gagarumin bukin da aka gudanar.

1613800
An rantsar da sabon Shugaban Kasar Nijar

A Yamai Babban Birnin Nijar, an rantsar da sabon Shugaban Kasar Mohamed Bazoum a gagarumin bukin da aka gudanar.

A bukin da aka gudanar a Babban Dakin Taro na Mahatma Gandhi da ke Yamai, shugabannin kasashen Afirka da dama sun samu damar halarta.

Mataimakin Shugaban Kasar Turkiyya Fuat Oktay ne ya wakilci kasarsa a wajen taron.

Ana sa ran Oktay zai yi ganawa da Shugabannin Nijar bayan kammala taron rantsuwar.

A zagaye na biyu na zaben da aka yi a ranar 21 ga Fabrairu, dan takarar jam'iyyar mai mulki ta PNDS-Tarayya Mohammed Bazoum ne ya yi nasara.Labarai masu alaka