Wata rikitacciyar cuta ta kwantar da dalibai 30 a Najeriya

Wata rikitacciyar cuta da ba a gano wacce irin ba ce ta kwantar da dalibai mata 30 a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

1608794
Wata rikitacciyar cuta ta kwantar da dalibai 30 a Najeriya

Wata rikitacciyar cuta da ba a gano wacce irin ba ce ta kwantar da dalibai mata 30 a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.

Kwamishinan Lafiya na jihar Sokoto Dr. Abdurrahman Dantsoho ya shaida cewa, abun takaici ne yadda wannan abu ya faru a makaranta.

Dantsoho ya ce, an aika da jami'an lafiya 10 zuwa makarantar, kuma an dauki ruwa da ciyayi da ke makarantar don gudanar da gwaje-gwaje.

Kwamishinan ya kara da cewa, ya zuwa yanzu babu wanda ya rasa ransa sakamakon lamarin.Labarai masu alaka