Turkiyya ta aike da sakon jaje ga Kamaru

Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga Kamaru sakamakon mummunan hatsarin motar da ya afku a garin Dschang tare da yin ajalin mutane da dama.

1573444
Turkiyya ta aike da sakon jaje ga Kamaru

Turkiyya ta aike da sakon jaje da ta'aziyya ga Kamaru sakamakon mummunan hatsarin motar da ya afku a garin Dschang tare da yin ajalin mutane da dama.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar da cewa, sun yi bakin cikin samun labarin mutuwar mutane 53 a ranar 27 ga Janairu.

Sanarwar ta ce "Muna jin radadin da jama'ar Kamaru suke ji sakamakon wannan ibtila'i. Muna Addu'ar samun jin kai ga wadanda suka mutu da sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata."

Mutane 53 ne suka rasa rayukansu, wasu 29 kuma suka samu raunuka sakamakon hatsarin da ya afku a mahadar Falaise da ke garin Dschang na Kamaru a lokacin da wata mota dauke da fasinjoji kusan 70 ta yi karo da wata motar a-kori-kura.Labarai masu alaka