'Yan tawayen CODECO sun kashe fararen hula 25 a Kongo

'Yan tawayen CODECO da ke jihar Ituri a arewacin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun kai hari tare da kashe fararen hula 25.

1452443
'Yan tawayen CODECO sun kashe fararen hula 25 a Kongo

'Yan tawayen CODECO da ke jihar Ituri a arewacin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo sun kai hari tare da kashe fararen hula 25.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na sun ce 'yan tawayen na CODECO sun kai hari da tsakar dare a yankin Dturgu na jihar Ituri.

Mutane 25 sun mutu sakamakon harin inda wasu 10 suka jikkata.

An bayyana kai wadanda suka jikkata zuwa Bunia Babban Birnin jihar Ituri.

Al'ummar yankin sun fara barin matsugunansu saboda rikicin da suke fuskanta na tsawon lokaci.Labarai masu alaka