An kashe 'yan Boko Haram da 'yan bindiga dadi kusan 200 a Najeriya

A Najeriya, an kashe 'yan ta'addar Boko Haram da 'yan bindiga dadi kusan 200 a mako dayan da ya gabata.

1452477
An kashe 'yan Boko Haram da 'yan bindiga dadi kusan 200 a Najeriya

A Najeriya, an kashe 'yan ta'addar Boko Haram da 'yan bindiga dadi kusan 200 a mako dayan da ya gabata.

Kakakin Ma'aikatar Tsaron Najeriya John Eneche ya shaida cewar dakarun sojin kasarsun kai farmakai kan 'yan ta'addar Boko Haram da 'yan bindiga dadi a jihohin Borno, Zamfara da Katsina.

Eneche ya ce a jihohin Zamfara da Katsina an kashe 'yan binciga 104 tare da jikkata wasu da dama daga cikinsu.

A farmakan da aka kaiwa 'yan ta'addar Boko Haram a dajn Sambisa kuma an kashe mambobin kungiyar 92, an kama wasu 4 da ransu inda aka lalata mafaka da maboyarsu.

Eneche ya kuma ce an kubutar da wasu mutane 34 da 'yan ta'addar suka yi garkuwa da su.

 Labarai masu alaka