Firaministan Ivory Coast ya kwanta dama

Firaministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya kwanta dama.

1451761
Firaministan Ivory Coast ya kwanta dama

Firaministan Ivory Coast Amadou Gon Coulibaly ya kwanta dama.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa a yayin zaman Majalisar Zartarwa a ranar Larabar nan ne Coulibaly ya sanar da ba ya jin dadi, kuma a watan Mayu ya je Faransa don a duba lafiyar zuciyarsa inda ya dawo kasarsa a ranar 2 ga watan Yuli.

An kai Coulibaly wani karamin asibiti mai zaman kansa a Abidjan Babban Birnin Kasar inda duk kokarin ceton ransa da aka yi ya ci tura.

Coulibaly da yake dan takarar jam'iyyarsa a zaben Shugaban Kasar da za a yi a ranar 30 ga watan Oktoba, a watan Maris ya yi mu'amala da wani mai dauke da cutar Corona, amma bayan yi masa gwaji sau 2 aka bayyana ba ya dauke da cutar.

A watan Mayu Coulibaly mai shekaru 61 ya je Faransa don duba lafiyarsa inda aka bayyana masa cewar an samu wani datti a zuciyarsa, kuma likitoci suka bukaci da ya kwanta don ya huta.Labarai masu alaka