Ebola ta yi ajalin karin mutane 18 a Kongo

Mutane 18 sun sake rasa rayukansu sakamakon barkewar annobar Ebola a karo na 11 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

1451824
Ebola ta yi ajalin karin mutane 18 a Kongo

Mutane 18 sun sake rasa rayukansu sakamakon barkewar annobar Ebola a karo na 11 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Jami'an yaki da annobar Ebola sun bayyana cewar karin mutane 6 sun sake kamuwa a jihar Equateur wanda ya kawo adadin masu dauke da cutar zuwa 43 a karo na 11 da ta barke a kasar, kuma wasu karin mutane 3 sun mutu wanda hakan ya kawo adadin wadanda suka rasa rayukansu zuwa mutane 18.

Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ta bayyana cewar a a watan Yuni ne karo na 10 na annobar Ebola da ya faro a 2018 ya kawo karshe a kasar.

 Labarai masu alaka