Dakarun Libiya sun yi babban nasara akan mayakan Hafter

Dakarun kasar Libiya sun yi nasarar kakkabe mayakan Hafter daga jihar Terhune daga gabashin kasar tare da karbe ikon yankin baki daya

1430055
Dakarun Libiya sun yi babban nasara akan mayakan Hafter

Dakarun kasar Libiya sun yi nasarar kakkabe mayakan Hafter daga jihar Terhune daga gabashin kasar tare da karbe ikon yankin baki daya.

Dangane da sanarwar da rundunar sojan kasar Libiya ta fitar a rubuce sojojin kasar sun kalubalanci mayakan Hafter a yankunan hudu tare da yin nasarar karbe ikon tsakiyar jihar Terhune.

Sanarwar ta kara da cewa dakarun na Libiya sun yi nasarar kame daya daga cikin jagororin mayakan Hafter a garin Terhune mai suna Riyad el-Kubeyyir.

Haka kuma dakarun kasar sun kaiwa mayakan Kaniyat farmaki wadanda keda alaka da mayakan ta Hafter.

Mayakan da ke da alaƙa da Hafter su na amfani da garin Terhune dake kudu maso gabashin kasar mai tazarar kilomita 90 zuwa babban birnin Tripoli, wajen kai farmakai a babban birnin kasar.

 Labarai masu alaka