AfDB ya amince da gudanar da bincike mai zaman kansa akan Adesina

Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya amince da gudanar da bincike mai zaman kansa a kan shugabansa Akinwumi Adesina, wanda ake zarge-zargen aikata rashawa da kuma nuna ɓangaranci

1430284
AfDB ya amince da gudanar da bincike mai zaman kansa akan Adesina

Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya amince da gudanar da bincike mai zaman kansa a kan shugabansa Akinwumi Adesina, wanda ake zarge-zargen aikata rashawa  da kuma nuna ɓangaranci.

Kamar yadda kwamitin bankin na AfDB ya sanar, kwamitin ya amince da gudanar da bincike mai zaman kansa akan shugaban bankin Adesina akan zarge-zargen da ake yi masa na aikata rashawa da nuna fifiko.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar mai zaman kanta da za ta gudanar da binciken zata kasance wacce bata da alamar tambaya ko kadan.

An zarge-zargen cewa Adesina ba tare da bin ka'idojin bankin ba ya nuna bangaranci da fifiko ga wasu abokansa da 'yanuwansa daga cikin ma'aikatan bankin wadanda ba'a bayyana sunayensu ba.

Amurka wacce ita ce ta biyu mafi yawan hannun jari a bankin bayan kasar Najeriya ta fito karara ta bayyana cewar bata yadda da wanke Adesina da akayi akan laifukan da ake zarginsa ba.

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna goyon bayansa ga Adesina wanda zai sake neman wa'adin cigaba da jagorancin bankin a watan Agusta duk da zarge-zargen da ake yi masa.

Shugaban bankin Adesina dai ya musunta dukkanin zarge-zargen da ake yi masa.

 Labarai masu alaka