Turkiyya ta aike sakon ta'aziyya ga Najeriya

Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Najeriya sakamakon mutanen da aka kashe a hare-haren ta'addanci a kasar.

1420902
Turkiyya ta aike sakon ta'aziyya ga Najeriya

Turkiyya ta aike da sakon ta'aziyya ga Najeriya sakamakon mutanen da aka kashe a hare-haren ta'addanci a kasar.

Rubutacciyar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajea ta Turkiyya ta fitar ta ce, sun yi matukar bakin ciki da samun labarin kashe mutane a hare-haren ta'addancin da aka kai a jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Sanarwar ta ce "Muna sukar wadannan munanan hare-hare na ta'addanci. Muna Addu'ar samun jin kan Allah ga wadanda suka mutu da saukin cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata. Muna mika ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar Najeriya baki daya.

Mutane 20 aka kashe yayinda wasu da dama suka samu raunuka sakamakon hare-haren da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso-gabashin Najeriya.Labarai masu alaka