'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 20 a Najeriya

Mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso-gabashin Najeriya.

1420682

Labaran da jaridun Najeriya suka fitar sun ce 'yan ta'addar sun kai hari a kauyen Gajigana na jihar Borno inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

An bayyana mutuwar mutane 20 tare da jikkatar wasu da dama sakamakon harin.

A harin da 'yan ta'addar suka kai a yankin Dapchi na jihar Yobe kuma sun kona gidaje tare da diban kayan abinci.

A wasu farmakai da dakarun Najeriya suka kai wa 'yan ta'addar Boko Haram a ranar Litinin din da ta gabata a jihar Borno sun kashe mambobin kungiyar 20.Labarai masu alaka