An kashe mutane 38 a rikicin kabilanci a Najeriya

Akalla mutane 38 ne suka rasa rayukansu sakamakon rikicin kabilanci da ya afku tsakanin wasu kabilu 2 a jihar Adamawa da ke arewa maso-gabashin Najeriya.

1419279

An bayyana jikkata mutane da dama da kona gidaje da yawa sakamakon rikicin.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Adamawa Sulaiman Nguroje ya gasgata afkuwar rikicin amma bai ce komai ba game da adadin wadanda aka kashe.

Nguroje ya bayyana cewar sun aike da jami'an tsaro zuwa yankin, kuma an shawo kan lamarin.

Ana yawan samun rikici kan gonaki da iyaka a tsakanin kabilun jihar Adamawa wanda ke janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

 Labarai masu alaka