Mutane dubu 500 na fuskantar barazana daga yunwa a Zimbabwe

Akalla mutane dubu 500,000 ne suke fuskantar barazana daga yunwa a Zimbabwe dake kudancin Afirka.

1394789
Mutane dubu 500 na fuskantar barazana daga yunwa a Zimbabwe

Akalla mutane dubu 500,000 ne suke fuskantar barazana daga yunwa a Zimbabwe dake kudancin Afirka.

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ta bayyana cewar kusan rabin jama'a kasar Zimbabwe ba sa samun abinci isasshe kuma akalla mutum dubu 500 na fuskantar mummunar barazana daga yunwa.

Daraktan WFP a Zimbabwe Eddie Rowe ya shaida cewar mafi yawan jama'ar kasa na gwagwarmaya da yunwa, kuma adadin masu bukatar cimaka a kasar ya karu daga miliyan 3.8 a bara zuwa miliyan 4.3 a bana.

Rowe ya ce ya zama wajibi a dauk matakan riga-kafi a kasar don magance abunda ka iya zuwa ya komo.

Ya ce "Dole ne mu yi duk mai yiwuwa don magance wannan bala'i."Labarai masu alaka