An kashe daya daga cikin manyan jagororin Al-Shabab a Somaliya

An bayyana cewar Amurka ta kai wasu farmakai ta sama a Somaliya tare da kashe daya daga cikin manyan jagororin kungiyar ta'adda ta Al-Shabab.

1393268

Ofishin Dakarun Amurka na Afirka (AFRICOM) ya fitar da rubutacciyar sanarwa cewa, a ranar 2 ga watan Afrilu an kai hare-hare ta sama a yankin Bay, wanda bayan haka ne aka gano an kashe daya daga cikin manyan shugabannin Al-Shabab Yusuf Jiis.

Sanarwar ta rawaito Kwamandan AFRICOM Janaral Stephen Townsend na cewa dan ta'addar da aka kashe ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba kuma "Daya daga cikin mutane masu muhimmanci ne a shugabancin Al-Shabab."

Wata sanarwa ta daban da aka fitar daga ofishin ta ce a hare-haren da aka kai a kauyen Jiib an kashe 'yan ta'addar Al-Shabab 5.Labarai masu alaka