Dakarun gwamnatin GNA ta karbe ikon yammacin Tripoli a Libiya

Dakarun gwamnatin yarjejeniya ta kasa (GNA) a Libiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun karbe ikon dukkanin yankin kudu masu yammacin Tripoli da kuma yankin Vatiyye mai muhinmanci

1384998
Dakarun gwamnatin GNA ta karbe ikon yammacin Tripoli a Libiya

Dakarun gwamnatin yarjejeniya ta kasa (GNA) a Libiya karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun karbe ikon dukkanin yankin kudu masu yammacin Tripoli da kuma yankin Vatiyye mai muhinmanci.

Gwamnatin GNA ta fara Farmakin Guguwar Zaman Lafiya a safiyar jiya lamarin da kwamandan farmakin Janar Usame Juveyli ya sanar a rubuce inda ya kara da cewa dakarun sojojin zasu karbe dukkanin ikon sararin samaniyyar yankin.

Juveyli, ya kara da cewa duk da kiran da MDD ta yi na a tsagaita wuta domin kara samun damar yaki da cutar coronavirus mayakan Hafter na ci gaba da kai hare-hare a yankin Tripoli.

Ya kara da cewa a farmakin da aka fara safiyar jiya an karbe dukkani ikon yankunan baki daya daga hannun mayakan Janar Hafter.

A watan Agustus din shekarar 2014 ne mayakan Hafter suka karbe ikon sansanin dake kusa da filin tashi da saukar jiragen saman Mitiga mai suna Vatiiye. Dakarun gwamnatin GNA ta karbe ikon yankin a watan Afirilun shekarar 2019 na dan wani lokaci daga bisani kuma suka rasa.

 Labarai masu alaka