'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 92

Sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a kasar Chadi dake Tsakiyar Afirka an kashe jami'an soji 93 tare da jikkata wasu 47.

1384524
'Yan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi 92

Sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a kasar Chadi dake Tsakiyar Afirka an kashe jami'an soji 93 tare da jikkata wasu 47.

A sanarwar da Shugaban Kasar Chadi Idris Derby ya fitar a lokacinda ya ziyarci yankin da aka kai harin ya ce an dauki tsawon awanni 5 ana musayar wuta tsakanin 'yan ta'addar Boko Haram da sojoji a sansanin soji na jihar Bouma.

Shugaba Deby ya ce "An kashe akalla sojoji 92 tare da jikkata wasu 47. A karon farko mun rasa sojoji masu yawa. Kuma za mu mayar da martani mummuna ga harin."

Labaran da jaridun kasar suka fitar sun ce a harbo jirgin saman sojin Chadi da aka aika don bayar da taimako a lokacinda arangamar ta barke.

Dakarun sojin Chadi sun sanar da kwace iko da yankin baki daya.

A Najeriya kuma a cikin mako dayan da ya gabata an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 50 a hare-haren da aka kai a arewa maso-gabashin Najeriya.

Kakakin Ma'aikatar Tsaro ta Najeriya John Enenche ya shaidawa 'yan jaridu cewar a mako dayan da ya gabata an kai wa 'yan ta'addar Boko Haram hare-hare a Gwoza da Yamteke dake jihar Borno.

Enenche ya ce an kashe 'yan ta'adda 50 a hare-haren inda wasunsu da dama suka tsere da raunukan da suka samu. An kuma kwace makamai da yawa daga hannunsu.

Enenche ya kara da cewar an jikkata sojoji 4 a yayin kai farmakan.Labarai masu alaka