Mayakan Haftar sun kashe 'yan mata 2 a Libiya

Sakamakon harin bam da mayakan dan juyin mulki Haftar Khalifa suka kai a kudancin Tarabulus Babban Birnin Libiya 'yan mata 2 sun rasa rayukansu.

1383812
Mayakan Haftar sun kashe 'yan mata 2 a Libiya

Sakamakon harin bam da mayakan dan juyin mulki Haftar Khalifa suka kai a kudancin Tarabulus Babban Birnin Libiya 'yan mata 2 sun rasa rayukansu.

Gidaje 2 ne suka rushe a yankin Hallet Al-Nur na Tarabulus sakamakon harin na mayakan Haftar inda aka ciro jikkunan 'yan mata 2 daga karkashin kasa.

Kakakn Rundumnar Sojin gwamnatin Sulhun Kasa ta Libiya Laftanal Kanal Muhammad Kununu ya fitar da sanarwa ta shafin Facebook din "Farmakan Fushin Dutse Mai Aman Wuta" inda ya ce mayakan Haftar sun kai hare-hare a cikin awanni 48 da suka gabata, sun kashe mutane 6 tare da jikkata wasu 6.

Kakakin 'yan tawaye masu goyon bayan Haftar Ahmad Al-Mismari a ranar 21 ga Maris ya shaidawa 'yan jaridu cewa sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya da Turai suka nema cimma a kasar saboda yaki da cutar Corona.

Amma duk da wannan yarjejeniya mayakan na Haftar na ci gaba da kai wa Tarabulus hare-hare.Labarai masu alaka