An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 50 a Najeriya

A cikin mako dayan da ya gabata an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 50 a hare-haren da aka kai a arewa maso-gabashin Najeriya.

1384073
An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 50 a Najeriya

A cikin mako dayan da ya gabata an kashe 'yan ta'addar Boko Haram 50 a hare-haren da aka kai a arewa maso-gabashin Najeriya.

Kakakin Ma'aikatar Tsaro ta Najeriya John Enenche ya shaidawa 'yan jaridu cewar  mako dayan da ya gabata an kai wa 'yan ta'addar Boko Haram hare-hare a Gwoza da Yamteke dake jihar Borno.

Enenche ya ce an kashe 'yan ta'adda 50 a hare-haren inda wasunsu da dama suka tsere da raunukan da suka samu. An kuma kwace makamai da yawa daga hannunsu.

Enenche ya kara da cewar an jikkata sojoji 4 a yayin kai farmakan.Labarai masu alaka