Mayakan Haftar sun kashe mutum 1 a Libiya

Mutum 1 ya rasa ransa sakamakon hari da 'yan tawayen dake biyayya ga dan juyin mulki Haftar Khalifa suka kai a Libiya.

Mayakan Haftar sun kashe mutum 1 a Libiya

Mutum 1 ya rasa ransa sakamakon hari da 'yan tawayen dake biyayya ga dan juyin mulki Haftar Khalifa suka kai a Libiya.

Sanarwar da aka fitar daga ofishin yada labarai na farmakan "Bacin Ran Dutse Mai Aman Wuta" da gwamnatin sulhun kasa ta Libiya ke kai wa ta ce, mayakan Haftar sun kai hari da makamin roka kan gidajen fararen hula a kudu maso-yammacin birnin Tarabulus.

Mutum 1 ya mutu yayinda wasu 9 suka jikkata sakamakon fadowar makamin rokar da aka harba kan wani gidan shan shayi.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Turkiyya da Rasha suka sanya hannu a kai a ranar 12 ga watan Janairu, amma bangarorin da ke rikici da juna a Libiya na ci gaba da arangama da kai hare-hare.Labarai masu alaka