An kashe mutane dubu 3,188 a shekarar 2019 a Najeriya

Wani rahoto da aka fitar ya bayyana cewar an kashe mutane kimanin dubu 3,188 sakamakon arangama da rikice-rikicen da aka fafata a Najeriya a shekarar 2019 da ta gabata.

Wakilin Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa ta Najeriya Chidi Odinkalu ya fadi cewar a jihar Borno dake yankin arewa maso-gabashin Najeriya ne aka fi samun arangamar.

Odikanlu ya ce a Najeriya baki daya a 2019 an kashe mutane dubu 3,188 da suka hada da fararen hula 2,707 da jami'an tsaro 481.

Ana samun asarar rayukaa Najeriya sakamakon rikicin Boko Haram da na manoma da makiyaya.Labarai masu alaka