Mayakan sa kai sun kashe 'yan ta'adda 14 a Burkina Faso

Mayakan sa kai da gwamnati ta amince da su a watan da ya gabata a Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda 14 da suka kai hari kauyukan arewa ta tsakiyar kasar.

Shafin yanar gizo na Infowakat ya rawaito wata majiyar jami'an tsaro na cewa wasu da ba a san ko su waye ba ne suka kai hari kauyukan Basse, Nafo, Abra da Tebra da ke garin Bourzanga

Sakamakon martanin da mayakan na sa kai suka mayarwa da maharan, an kashe 'yan ta'adda 14, 'yan sa kai 2 da fararen hula 2. An kuma jikkata wani farar hula 1.

A gefe guda kuma sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda 7 a lokacinda suka kai wa shingen binciken ababan hawansu hari a garin Tanwalbougou na gabashin kasar.

Haka zalika mayakan na sa kai sun kashe 'yan ta'adda 22 a ranar Juma'ar makon da ya gabata a yayinda suka kai hari a yankin Soum na arewacin Burkina Faso.

A watan da ya gabata ne Majalisar Dokokin Burkina Faso ta tabbatar da dokar amincewa da mayakan sa kai a kasar da su dauki makamai tare da yakar ta'addanci.Labarai masu alaka