'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 30 a Najeriya

Mutane 30 sun rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai wa wasu motoci da suka tare a kan hanyarsu ta zuwa Maiduguri dage arewa maso-gabashin Najeriya.

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya fadi cewar an kashe mutane 30 a harin.

Wani direban mota ya shaida cewa 'yan ta'addar sun rufe hanyar Damaturu-Maiduguri tare da bude wuta kan jama'a.

An kona ababan hawa da dama sakamakon harin.Labarai masu alaka