Me ya sa kasashen Afirka suka kasa yin tasiri a kokarin samar da zaman lafiya a Libiya?

Za mu gabatar muku da sharhin da dalibi mai bincike dake karatun digirgir a jami’ar Bayreuth Ibrahim Bachir Abdoulaye.

Me ya sa kasashen Afirka suka kasa yin tasiri a kokarin samar da zaman lafiya a Libiya?

Tsoma hannun da aka yi a Libiya a shekarar 2011, hakan ya janyo babban rikici a yankin Sahel dake Afirka tare da kawo wani rikicin na masu neman mafaka da gudun hijira a Turai. A baya kasar da ake wa kallon na da kyau da damarmaki, ta zama babban bala’i ga ‘yan Afirka sakamakon yakin basasar da ta fada. Libiya dake da arzikin man fetur ta kasance tana samar da aiyuka ga dubunnan mutane dake fitowa daga yammacin Afirka. Sannan sojojin haya da Gaddafi ya dauka daga kasashe makota na samar da karin arziki ga kasashensu. Amma a lokacinda gwamnatin Gaddafi ta fadi kuma kasar ta fada yakin basasa, sai hakan ya zama mafarar rikici ga kasashe masu rauni makotan Libiya kamar su Nijar da Mali. Komawar sojojin Tuareg zuwa kasashensu da makamansu ya yi tasiri wajen ruruwar rikicin da ake yi a Mali.

A lokacinda rikicin Libiya ya zamo matsalar tsaro ga kasashen Afirka, ya kuma bude hanyar rikicin ‘yan gudun hijira a Turai. Dubunnan ‘yan Afirka masu gudun hijira da suke zaune a Libiya babu aiyukan yi, duk da barazanar mutuwa amma sun dinga bin hanyar teku don zuwa Turai. Matasa da suka gujewa rikicin da ake yi a kasashensu na shiga hadarin zuwa Turai ta Libiya inda suke bi ta teku. Sakamakon yadda Libiya ta hada Yammacin Afirka da tekun Bahar Rum, ta zama babbar hanyar masu son tafiya Turai. A yarjejeniyar da Nijar da Turai sukaamince da ita don kafa sansanin masu gudun hijira a Agadez, sun so yin kokarin ganin sun dakile lamarin daga kasar. Wannan yanayi ya janyo take hakkokin dan adam da suka hada da cinikin mutane da fataucinsu. Labaran da kafafan yada labarai ke fitarwa na cewa dubunnan mutane sun fada hannun ‘yab tawaye masu fataucin mutane.

Da an ayi amfani da shawarar da Tarayyar Afirka ta bayar don kawo karshen rikicin Libiya, to da ba a kawo wannan gaba ba ta rikicin kasar ba. Tarayyar Afirka da ta yi gargadin da aka ki aiki da shi game da Libiya, a shekarar 2011 ta nuna rashin amincewa game da afkawa Libiya da aka yi. Tun farkon fara rikicin na Libiya Tarayyar Afirka ta ce, abun zai illata kasashe makota. Tarayyar Afirka ta yi kokarinta na kawo karshen rikicin Libiya da ya faro bayan afkawa kasar da Amurka, Faransa da Ingila suka yi, amma ba ta yi nasara ba. Rikicin Libiya ya zama kamar wani rikici na kasashen waje da suke yi ta hanyar wakilci. Libiya dake da arzikin mai a mataki na 4 a Afirka bayan Najeriya, Angola da Aljeriya, tana cikin kasashen duniya 10 dake fitar da albarkatun man fetur. Hakan yasa kasashe irin su Faransa da Rasha suke goyon bayan dan juyin mulki Haftar Khalifa inda suke son kasar ta sake fadawa hannun dan kama karya yadda za su dinga diban arikin mai. Amma taimakon da Turkiyya ta ba wa gwamnatin hadin kan kasa ta Tarabulus ya hana Haftar kwace babban birnin. Shigar Turkiyya Libiya ya sake hanzarta kokarin kawo zaman lafiya a kasar. Ta hanyar kokarin Turkiyya dukkan bangarorin dake Libiya da masu goya musu baya sun yi taro a Berlin.

Yadda Masar ta dinga nuna hali da ya saba wa na Tarayyar Afirka game da Libiya, ta sake raunata yunkurin Tarayyar na neman samar da zaman lafiya a Libiya. A wani taro da Shugaban Tarayyar Afirka Mousa Faki, Shugaban Kasar Aljeriya Abdulmajid Tebbun da Shugaban Kasar Kongo kuma Shugaban Kwamitin Tarayyar Afirka Denis Sassou Nguesso suka halarta sun bukaci Tarayyar ta kawo karshen rikicin na Libiya. Amma shugaban kasar Masar Abdulfatah Al-Sisi dake taimakawa Haftar ya nuna ba ya goyon bayan yunkurin na Tarayyar Afirka don samar da zaman lafiya a Libiya. Hakan ya sanya kokarinta ya yi rauni matuka. Kuma yadda yake taka rawa a Majalisar Dinkin Duniya game da Libiya, ya sanya Tarayyar Afirka ta kasa samun wani katabus wajen warware rikicin na Libiya. Masar na ba wa Haftar dukkan taimako inda take son da ya karbi kasar ta kowacce hanya.

A watan Afrilu mai zuwa za a gudanar da taron Turkiyya-Afirka a Istanbul, za a iya kara karfafa alakar Turkiyya dake goyon bayan halartacciyar gwamnati a Libiya da Tarayyar Afirka. A karkashin haka, taron na Istanbul zai bayar da dama ga Turkiyya da kasashen Afirka su tattauna batututuwa masu muhimmanci irin su halin da ake ciki a Libiya.Labarai masu alaka