An gudanar da zanga-zangar kalubalantar kasancewar sojojin Faransa a Nijer

A nahiyar Afirka da ake ci gaba da kalubalantar tabi'ar kasashen yamma  a Nijer an gudanar da zanga-zangar kalubalanatar kasancewar sojojin Faransa a kasar

An gudanar da zanga-zangar kalubalantar kasancewar sojojin Faransa a Nijer

A nahiyar Afirka da ake ci gaba da kalubalantar tabi'ar kasashen yamma  a Nijer an gudanar da zanga-zangar kalubalanatar kasancewar sojojin Faransa a kasar.

A zanga-zangar da aka shirya a Niame babban birnin kasar ya samu halartar dinbin al'umman kasar, kasancewar yadda sojojin Nijer sunka yi rashi a yaki da ta'addanci ya sanya kiraye-kirayen cewa sojojin Faransa su fice daga kasar.

"Yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa wadanda ke tarzomar wadanda mafi yawansu matasa ne.

Matasan da sunka rinka mayar da martani ta hanyar jifar 'yan sandan da duwatsu sun kuma kone tayoyi a wasu gurare.

Wadanda suka jagoranci hada zanga-zangar sun bayyana cewa sun yi hakan ne domin kara wa sojojin kasar karfin gwiwar yaki da ta'addanci inda kuma suka bayyana cewa matukar sojojin Barkhane na Faransa na yankin Sahel kasashe yankin ba zasu taba kasancewa cikin 'yanci ba.

 Labarai masu alaka