An kashe malaman makaranta 3 a harin 'yan bindiga a Kenya

Malaman makaranta 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a wani yanki a Kenya dake kusa da iyakar kasar da Somaliya.

An kashe malaman makaranta 3 a harin 'yan bindiga a Kenya

Malaman makaranta 3 sun rasa rayukansu sakamakon harin 'yan bindiga a wani yanki a Kenya dake kusa da iyakar kasar da Somaliya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa na cewa wasu da ake zargin 'yan ta'addar Al-Shabab ne suka kai hari a garin Garissa dake gabashin Kenya inda suka kashe malaman makaranta 3.

Wani jami'in 'yan sanda da ya yi bayani ga manema labarai ya ce jami'ansu sun mayar da martani ga 'yan bindigar da suka nude wuta kan cibiyar 'yan sanda.

A wani hari da aka kai a makon da ya gabata a kasar an kashe fararen hula 4. A harin da Al-Shabab ta kai a sansanin Amurka kuma ta kashe sojan Amurka 1 da fararen hula Amurkawa 2.

Kungiyar Al-Shabab dake rike da kauyuka da dama kuma take da manufar kifar da gwamnatin Mogadishu, ta kai hari na 4 kenan a Kenya a wannan shekarar.Labarai masu alaka