'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 11 a Najeriya

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a yankin arewa maso-gabashin Najeriya.

'Yan ta'addar Boko Haram sun kashe mutane 11 a Najeriya

Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da 'yan ta'addar Boko Haram suka kai a yankin arewa maso-gabashin Najeriya.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa mambobin kungiyar ta'adda ta Boko Haram sun kai hari a yank,n Monguno na jihar Borno inda suka kashe mutane 11 da suka hada da sojoji 3.

'Yan ta'addar sun jikkata wasu mutanen da dama inda wasu da yawa suka bar matsugunansu.

A shekarun 2000 aka kafa Boko Haram inda ta fara kai hare-hare a shekarar 2009 kuma ya zuwa yau ta kashe sma da mutane dubu 20.

Daga shekarar 2015 zuwa kungiyar ta'adda ta Boko Haram ta kashe mutane akalla dubu 2 a yankin tafkin Chadi dake iyakar kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.

 Labarai masu alaka